GABATARWA:

TSANANI, TSANGWAMA DA HADARIN DA HAUSAWA MABIYAN ALMASIHU KE FUSKANTA

Da farko dai, Hausa yarene ba addini ba. Akasarin Hausa, na zaunene a arewacin Nigeria da sauran wasu kasashen Africa kamarsu; Niger, Benin, Ivory coast, Cameroon, Chad, Ghana, Sudan,Togo, Gbon, Algeria, Congo dakuma Burkina faso. Tunfil azal,Hausawa sun kasance yan Nigeria. Hausawa da yaran su, nanan tun kamin zuwan turwa da larabawa da suka kawo addini a Africa, kamar dai sauran harsuna da kabilai.
Wasu daga cikinsu sun karbi bisharar Almasihu. Wasu sun zama kristoci karkaashin almasihu. Wasu kuma suna nan cikin addinin gargajiya da suka gada daga kakanni,wato maguzanci. Harshen Hausa shine babban harshe da aka fi amfanin da shi a arewa. Akasarin Hausawa mabiyin Almasihu sana’ar su nomane da kiwo,ba ragwaye bane ko kadan! Wanan yasa basu kwallafa ransu ga aikin bature ba, asalima sai suka gwammace suyi aiki tukuru domin samarwa kansu abinci da abubuwan bukata ta hanyar noma da kiwo da suka gada tun tale-tale. Ba masu tagumi da gwiwar wani bane, balantana ayi masu gori, sai dai suna riko da kayarwar Ubangijinsu cewa “kada rago yaci abinci”. Tuni suka san lalaci ba abin arzaki bane.
A Nijeriya ta arewa, mawuyacin abune kayi kacibus da mabaraci ko mai aikin aika-aika cikin Hausawa mabiyan Almasihu! Basu yin bara ko banbadanci daga wannan ma’aikata zuwa wa wacen kamar wadansu.
Hausawa mabiyan Almasihu sun kasance saniyar ware, sakamakon tsana da tsangwamar da akayi ma su tun bayyanar musulinci da darewar mabiyansa kan karagar mulki a arewacin Nigeria. Yaran Hausa, ya rasa matsayin san a farko, a inda a yau, mutane ke masa mum-munan zato da fassara shi da wadansu ma’anoni daban-daban, a cikin gida Nigeria dama duniya baki daya.
Hakika, Kalmar Hausawa ta sami kanta cikin tsaka mai wuya! A inda da zarar an ambaci ta sai wasu suji tsoro don sun dauka ana maganar tashin hankali keta masu tsatsauran ra’ayin musulinci masu zakin addini, tsageru masu tsanantawa mabiyan Almasihu ko kuma, Kristoci, masu mugun aiki, da dai sauran mugayen ma’anoni marasa dadin ji a kunnuwan kirki. Wani abin takaici shine, da zarar wani mutumi ko wata mutumiyar kudanci, ko gabashi, ko yammacin kasarnan ya ko ta zama musulmi sai kawai a rika kiransa bahaushe, ko kuma a kirata bahaushiya, ko shi ko ita su rika kiran kansu hausawa. Sai kaga nan da nan sun dora kahon zuka ga garensu ko dabi’unsu na asali wai don kawai su masallata ne. Wannan yasa da zarar mutanen yama, kudu ko gabashin kasannan sunji bahaushe to daukansu kawai masallacine ko masallaciya. Da zarar kaji suna maganar Hausa ko Hausawa to nufinsu kawai masallatane. Lamarin bai tsaya anan kawai ba, hatta sauran kabilun dake zaune a Nigeria ta Arewa duk haka ake masu wannan kallon biyu ahun! Da haka aka samo kalamai irin su Hausawa, Hausa-Fulani, Arewa, da dai sauransu. Babbar illar abin sune, yanci da daukakar da falalar da Allah ya yiwa wadansu kabilu daba muslmaibane duk musulunci yayi masu shamaki. An maishe mu kamar yan gudun hijira, baki, marasa yanci a garuruwanan na haihuwa da kasarmu ta gado, wai don kawai mu ba musulmai bane. Mun sha wahala iri-iri, kakaninmu da wasu iyayenmu sun bautu da muguwar bauta abin har cikin karni na ashirin da daya.

Hakika tsanani da tsangwama, da hadarin da mabiyan Almasihu, wato Hausawa Kristoci  ke fuskanta a Nigeria yakai intaha.

GA WASU KALILAN DAGA CIKIN TSANANIN DA HAUSAWA MABIYAN ALMASIHU KE FUSKANTA A NIJERIYA:

BABBAN UMURNIN CIBIYAR HAUSAWA KRISTA TA NIGERIA (HAUSA CHRISTIANS FOUNDATION – HACFO)

Cibiyar Hausawa Krista, cibiya ce dake Hidimar Bisharar Almasihu a cikin Al’ummar Hausawa ta Nijeriya wadda ke da umurnin kwance sarkokin mugunta, kwance masu sarkiya, yantar da wadanda aka zalunta, da kuma kakkarya kowacce karkiya dake addabar Hausawa. Ubangiji Yahweh ya kiramu ne don mu sake gina tsofaffin kufanmu na da can, mu sake kafa tushen zuriya da yawa a cikin tafarkin Ubangji, mu kuma gyara abinda da ya lalace, da kuma sake gyaran gidajenmu.
Sanadiyar umurnin Cibiyar Hausawa Kristoci (Hausa Christians Foundation) shine mu karfafa, mu gina, mu kuma tsare dukan Hausawa Krista daga farmakin makiyanmu da kuma kyarketan duniyan nan, da kuma cigaba da isar da Bisharar Almasihu Mai Ceton Duniya ga sauran Hausawa wadanda basu sami ceto ba don suma su samu sulhu da Ubangiji Mahalicci Mai Rai wato Yahweh.

KUDIRINMU

Kawo bege ga wadanda suka karaya, Karfin hali ga wadanda ke jin tsoro, gabagadin kare Bangaskiyarmu a cikin Alsmasihu da kuma sake gina halin jajircewa a cikin dukan Hausawa Krista a Nijeriya da yadda zasu fuskanci gabansu ba tare da tsoro ko shakka ba, ta haka muke samar da ma’aikatan Ubangiji Maza da Mata domin kai Bisharar Almasihu ga daukacin Hausawa ta wajen yin hidimar sulhu da Ubangiji.

JIGON WANZUWARMU

Don mu zama murya da zata yantar da dukan Hausawa Kristoci a Nijeriya daga duk wani kangin zalunci da cin mutuncin bil’adama da kuma moriyar da ya wajjaba mu samu daga gwabnati kamar yadda duk wani dan Nijeriya ya kamata ya samu, ta haka zamu samar da kofar shiga dukan kasar Hausa da Bisharar Isa Almasihu.

MANUFARMU

Nunawa ko koma sanar da daukanci duniya cewa akwaimu anan Arewacin Nijeriya kuma mu yan kasane, Nigeria tamuce muma,  muna kuma tinkaho da kasancewarmu na Almasihu a Kristance. Karfafawa da kuma goyon bayan dukan Kristoci Hausawa da su fito fili su bayyana zaluncin da suke fuskanta a duk inda suke a zaune; da kuma ci gaba da jajircewar neman yancin aikata bangaskiyarmu ta Krista batare da tsangwamaba kamar dai yadda sauran yan kasa ke nasu badali mu ma a sakar man mara! Ta haka zamu kare, mu kuma gina Hausawa Krista, mu kuma ribato sauran da har yanzu basu san Almasihu ba.

AYYUKANMU

A KARSHE

Akubar da Hausawa Kristoci ke ciki da ayar da ake gasa mana a hanu ya samo asaline daga zabin bangaskiyar da mukayi ta Kristanci. Wato bayyana yarda ga Ubangijinmu Yahweh, Yesu Almasihu Murucin kan-duste kowa ya rasa ka yayi hannun riga da samun ceto! Bacin ranmu ne muci gaba da ganin ana wahalar da mutanen mu a Nigeria ta Arewa, amma cike mu ke da murna ganin dorewar mu a kan dutsen ceto ko da me zai taho! Muna godo abisan gwiwayinmu cewar wannan madun-dumin na mugunta da iblis ke amfani dan makantarda zuciya da idanun makwabtanma, da kuma wasu yan’uwanmu ya kawu!
Muna masu godiya ga Buwayi tare da bashi dukan daukaka domin gaba-gadin da muka samu daga gare Shi zuwa ga illahirin masubi na arewacin Nigeria masamman Hausawa Kristoci. Zai cigaba da tabbatar mana da farin cikinmu da kyakkyawan begen mu don mu chigaba da bunkasuwa har sai mun gagari dukkan tsara! Saboda Almasihu daukaka ta tabbata ga Wannan da Yake da ikon aikatawa fiye da dukkan abin da zamu roka, ko zamu zata nesa, wato aikawa ta karfin ikonsa da yake aiki a zucciyarmu. A gareshi dukkan daukaka a ikilisiya da kuma Almasihu har gaban dukkan zamanai. Amin(Afisawa 3:20-21)

KALMAR TUSHEN KAMANIN HAUSAWA KRISTA

Mu Hausawa ne, mu kuma Kristoci ne! Tunaninmu na Almasihu ne. Ruhun da ya ta da Yesu daga matattu na zaune a cikin mu. Ba mu da ruhun tsoro a cikinmu, amma sai dai na halin iko, da Kauna, da kuma halin nagartattun ayyuka. Ba ma jin kunyar Shaidar Ubangijinmu Yesu Kristi. Ba ma jin kunyar bishara, domin it ace ikon Allah mai kai kowanne mai bada gaskiya ga samun ceto.
Nigeria kasarmu ce ta gado, Arewa gadonmu ne, Hausa harshen mu ne da kuma yarenmu, Kristanci kuma shine zabin mu na gari na bangaskiya. Muna fahariya da yadda muke, da kuma abinda muke da shi; ALMASHIHU A CHIKINMU, BEGEN DAUKAKAR DA ZA’A BAYYANA.
Muddin muna a raye a Nijeriya, baza mu amunce da duk wani irin zalunci ba sadoda mu Kristoci ne. Ba zamu ci gaba da yin shuru ba. A kullayaumin, zamu ci gaba da fadin gaskiya cikin kowanne yanayi da kuma haskaka hasken Almasihu.
A Arewacin Nigeria a yau, mun zama tankar kamar abinda Littafi Mai Tsarki ya fada a cikin 2 Korantiyawa 4:8-14

Ana wahalshe mu ta kowacce hanya, duk da haka, ba a ci dunguminmu ba. Ana ruda mu, duk da haka bamu karai ba. Ana tsananta mana, duk da haka bamu zama yasassu ba. Ana fyada mu a kasa,  duk da haka ba a hallaka mu ba. Kullum muna a cikin hatsarin kisa, irin kisan da aka yi wa Yesu, domin a bayyana rayuwar Yesu ta gare mu. Wato muddin muna raye, kullum zaman mutuwa muke yi saboda Yesu, domin a bayyana ran Yesu ta wurin jikin nan namu mai mutuwa. Ta haka mutuwa take aikatawa a cikinmu.

Tun da yake muna da ruhun bangaskiya iri daya da na wanda ya rubuta wannan, “Na gasgata, saboda haka na yi magana,” to, mu ma mun gasgata, saboda haka muke magana. Mun sani shi wannan da ya ta da Ubangiji Yesu daga matattu, mu ma zai tashe mu albarkacin Yesu, ya kuma kawo mu a gabansa tare da dukan Masubi.

Amin!

BUKATAR BISHARA

GABATARWA

ME YA KAWO HAKA?

INA MAFITA?

GASKIYAR MAGANA

Matt 24:14 – “Za a kuma yi bisharar nan ta mulkin sama ko ina a duniya domin shaida ga dukan al’umai. Sa’annan kuma sai karshen ya zo”

KIDIDDIGA A DUNIYANCE (ABINDA BINCIKE YA NUNA A DUNIYA)

TARUN JAMA’A HAUSAWA

MAI YUWUWA NE